Koriya ta Arewa ta yi nasarar gwajin makami
April 24, 2016Talla
Kafofin yada labarai na kasar ta Koriya ta Arewa dai sun ruwaito cewa shugaba Kim Jong-Un ya ce daga yanzu a ko yaushe kasarsa na iya harar biranen Seoul na Koriya ta Kudu da na Washington a Amirka a duk lokacin da ta yi niyar yin hakan.
Sai dai ministan tsaron Koriya ta Kudu ya bayyana cewa gwajin makamin da Koriya ta Arewar ta yi a wannan Asabar bai yi nasara ba, domin kuwa makamin ya fadi ne a cikin ruwan tekun Japan wanda ke nufin cewa bai wuce tafiyar nisan kilomita 30 ba da ya fadi.
Amirka da Birtaniya dai sun yi tir da Allah wadai da gwajin makamin wanda suka ce ya keta haddin kudirin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya haramta gwajin makami mai linzami.