Koriya ta arewa tace babu gudu babu ja da baya
October 5, 2006NKOREA/JAPAN................
Koriya ta arewa tace babu gudu babu jada baya, a game da shirin ta na gwajin makamin nukiliya.
Koda yake kasar ta koriya ta Arewa bata bayar da sanarwar sahihiyar rana ko wata ba a game da wannan shiri,to amma ta tabbatar da cewa shirin na nan daran kuma zata aiwatar dashi.
A cewar mahukuntan na Pyongyang zasu dakatar da wannan niyar ne kawai, idan Amurka ta canza takunta ga kasar ta koriya ta arewa ne.
Tuni dai kasashe masu fada aji a duniya suka gargadi kasar ta koriya ta arewa da kada ta aiwatar da wannan mataki, bisa hasashen cewa abu ne da zai kawo barazana ga harkokin tsaron yankin da kuma ma duniya baki daya.
Bayanai dai sun shaidar da cewa a yanzu haka Mdd na tattaunawa akan batun don sanin matakin daya kamata ta dauka na irin martanin da zata mayarwa koriya ta arewan.