1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa tayi gwajin Makamai.

July 4, 2009

Martanin Ƙasashen Duniya kan gwajin makamin Koriya ta Arewa

https://p.dw.com/p/IhF3
Shugaba Kim Jong Il, na Koriya ta arewaHoto: AP


Ƙasashen duniya daban daban na ci gaba da mayar da martani, game da gwajin makamai masu linzami - har guda bakwai ɗin da ƙasar Koriya ta arewa ta yi a wannan asabar, inda Amirka ta buƙaci mahukunta a birnin Pyongyang na Koriyar, dasu guji dagula yanayin zaman ɗar-ɗar a yankin.

Kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Amirka, Karl Duckworth, ya bayyana cewar, Amirka tana sanya ido sosai akan ayyukan da koriya ta arewa ke gudanarwa, da kuma ƙudurorinta, kana ya buƙaci koriya ta arewa ta nisanta kanta daga duk wani abinda zai ƙara tada jijiyar wuya a yankin, ta kuma mayar da hankali ga ƙoƙarin komawa ga tattaunawar kwance ɗamarar Nukiliyarta.

Su kuwa ƙasashen Rasha da China, bayyana gamsuwa suka yi da cewar, babu wani zaɓin daya fi tattaunawar nan ta ɓangarori shida akan dakatar da shirin Nukiliyar koriya ta arewa, kamar yanda ma'aikatar kula da harkokin ƙetaren Rasha ta sanar a wannan asabar, bayan ganawar da jami'an ma'aikatar suka yi, tare da Jami'an ƙasar China.

Mehr als 20 Tote bei Havarie auf russischem Atom U-boot
Hoto: picture-alliance / dpa

Ma'aikatar kula da harkokin tsaron Koriya ta kudu, ta bayar da tabbacin cewar, koriya ta arewa, ta yi gwajin makamai masu linzamin dake da nisan zango - har guda bakwai ta tekun ƙasar, lamarin da kakakin ma'aikatar kula da harkokin wajen Koriya ta kudu, Yonhap ya kwatanta da cewar, yin karan tsaye ne ga kudurin kwamitin sulhun majalisar ɗinkin duniya.

Itama ma'aikatar kula da harkokin wajen Japan, ta mayar da martanin dake yin Allah Wadai da gwajin makamai masu linzamin, tana mai bayyana hakan da cewar, neman tsokana ne ga ƙasashen dake makwabtaka da ita a yankin.

A nashi ɓangaren, wani babban hafsan rundunar sojin Amirka, wanda ke riƙe da muƙamin Admiral, wato Gary Roughead, wanda kuma a halin yanzu ke yin ziyara a ƙasar Japan, ya ce takunkumin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanyawa Koriya ta arewa a halin yanzu suna yin ta'asiri, sakamakon juya akalar wani jirgin ruwar dake ɗauke da makamai, wanda kuma ya fito daga koriya ta arewa:

Großbritannien Tony Blair legt Weißbuch zu nuklearer Streitkraft vor
Hoto: picture-alliance/ dpa

" Na yi amannar cewar, abinda muke gani a yanzu, shi ne ta'asirin kudurin kwamitin sulhun majalisar ɗinkin duniyar da aka fara yin aiki dashi, wanda kuma ya haramtawa wannan jirgin ruwa tafiya ko ina, domin ɗaukar mai ko kuma ruwa"

Gwajin makamai masu linzami guda bakwai masu nisan zango, ƙirar Scud, da koriya ta arewa ta yi a wannan asabar, shi ne mafi yawan da ta taɓa yi tun a shekara ta 2006, kana zai iya kaiwa zuwa ƙasashen China da Rasha, da Japan , da kuma Koriya ta kudu.

Duk da cewar, ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya ya buƙaci ƙasashe su bincike jiragen dake zuwa ko kuma ficewa daga koriya, ƙasar ta ce, zata ɗauki tsare jirginta a matsayin takalar yaƙi.


Mawallafi: Umar Saleh Saleh

Edita: Zainab Mohammed