1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta yi wa Amirka barazana

Abdul-raheem Hassan
January 20, 2022

Gwamnatin Koriya ta Arewa ta nuna alamun dawo da gwajin makaman nukiliya masu cin dogon zango, wannan mataki ne na martanin takunkumin da Amirka ta sa mata kan sake gwajin nukiliya.

https://p.dw.com/p/45oHo
Nordkorea | Raketentest
Hoto: KCNA/REUTERS

Tun a shekarar 2017 gwamnatin Pyongyang ba ta sake gwajin makami mai linzami ba, sakamakon ganawar Shugaba Kim Jong Un da stohon Shugaban Amirka Donald Trump har sau uku kafin tattaunawar ta ruguje bayan shekaru biyu.

Yiwuwar sake yin gwajin makaman nukiliya da makamai masu linzami masu cin dogon zango da za su iya kai wa Amirka hari, na zuwa ne a wani mawuyacin lokaci a yankin Koriya, inda babbar kawar Shugaba Kim wato kasar Sin za ta karbi bakwancin gasar Olympics ta lokacin sanyi a wata mai zuwa.