Koriya ta Kudu da China na taro kan tsaro
January 15, 2016Talla
Manyan jami'an hukumomin tsaro na kasashen Koriya ta Kudu da China sun soma wani zaman taro a wannan Jumma'a a birnin Seoul domin tattauna batun harkokin tsaro a kasar Koriya ta Kudu dama a yankin baki daya.
Ana sa ran a wannan karo taron wanda kasashen biyu suka saba gudanarwa a ko wace shekara zai mayar da hankali ne kan batun gwajin na hudu na makamin nukliya da Koriya ta Arewa ta gudanar yau da 'yan kwanaki.Lamarin da ya fiskanci suka daga kasashen duniya daban-daban a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi barazanar daukar sabbin matakan saka takunkumi ga kasar ta Koriya ta Arewa.