1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Kudu na atisayen sojoji

September 26, 2023

Matakin na zuwa ne kusan shekaru 10 da Koriya ta Kudun ke kauce wa nuna karfinta na yaki a duk lokacin da ranar wannan biki da ake gudanarwa a duk bayan shekara biyar ta zagayo.

https://p.dw.com/p/4Wnwh
Hoto: Yonhap/picture alliance

Koriya ta Kudu ta shirya gudanar da kasaitaccen faretin sojoji na nuna makaman da ta mallaka a wannan Talata.

A babban atisayen na bana, hukumomin Seoul sun shirya nuna faretin sojoji wajen 7,000 tare da baje kolin manyan makaman yaki wajen 350. Akwai kuma jiragen yaki maras matuka da su ma Koriyan ta Kudu za ta nuna, a wani abu da ke zuwa daidai lokacin da lokaci zuwa lokaci makwabciyarta Koriya ta Arewa mai makamin nukiliya ke shirya irin wannan atisaye.

Shugaba Yoon Suk Yeol da ya hau karagar mulki a shekarar da ta gabata na ci gaba da kokarin kulla alaka da Amirka, a wani mataki da ya ce yunkuri ne na kare kasarsa daga barazanar kai mata hari da makwabciyarta Koriya ta Arewa ke yi.