Koriya ta Kudu ta koma farfagandar kan iyaka
January 8, 2016Talla
Koriya ta Kudu ta koma a wannan Jumma'a gudanar da farfaganda da take yi da manyan Lasifikoki kan iyaka da takwararta ta Arewa a matsayin martani ga gwajin makamin nukliya na baya-bayan nan da Koriya ta Arewar ta gudanar.Koriya ta Kudu ta koma gudanar da farfagandar ce, wacce ga al'ada ke bakanta wa hukumomin Koriya ta Arewa da rai a wannan rana ta zagayowar cikon shekaru 32 da haifuwar Shugaban Koriya ta Arewar Kim Jong-Un.
A cikin watan Agusta na shekarar bara ne hukumomin Koriya ta Kudun suka kwance lasifikokin farfagandar tasu a sakamakon wata yarjejeniyar neman sasanta kasashen guda biyu da suka kusa kai ga gwabza fada a sakakamakon wannan farfaganda ta kan iyaka.