1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Kudu ta tsige sabon shugaban kasar

December 27, 2024

'Yan majalisar dokokin Koriya ta Kudu sun kada kuri'ar tsige mukadashin Shugaban kasar, Han Duck Soo, makwanni bayan tsige tsohon shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/4ocrG
Majalisar dokokin Koriya ta Kudu ta kada kuri'ar tsige mukadashin Shugaban kasar
Majalisar dokokin Koriya ta Kudu ta kada kuri'ar tsige mukadashin Shugaban kasarHoto: Ahn Young-joon/AP Photo/picture alliance

Tsige mukadashin Shugaban kasar Koriya ta Kudu, Han Duck Soo na zuwa ne makwanni biyu bayan tsige tsohon shugaban kasar, Yoon Suk Yeol daga mukaminsa sakamakon ayyana wata dokar soji ta wucin gadi. Kimanin 'yan majalisar 192 ne daga bangaren adawa da ke da rinjaye a majalisar suka kada kuri'ar sauke sabon shugaban daga kujerarsa. Babban jami'yyar adawa a kasar ta Democratic Party ta zargi Han da jan kafa wajen gudanar da bincike kan Shugaba Yoon da kuma hana aiwatar da tsige shi.

Karin bayani: Ana shirin tsige shugaban Koriya ta Kudu

A ranar Juma'ar ce kotun kundin tsarin mulkin Koriya ta Kudu za ta fara shari'a kan tsige tsohon shugaban kasar. Ana kuma sa ran nan da makwanni masu zuwa, kotun ta tabbatar da cewa ko majalisar dokokin kasar ta bi doka wajen tsige Shugaba Yoon. Idan har alkalan suka tabbatar da ingancin tsige shi, za a gudanar da sabon zabe a kasar zuwa nan da kwanaki 60. Idan kuma kotu ta yanke hukunci da ya kasance akasin hakan, Shugaba Yoon zai koma kan kujerarsa ta mulkin kasar ta Koriya ta Kudu.