Koriya ta Kudu ta yi kashedi ga ta Arewa
February 24, 2016Hukumomin sojan Koriya ta Kudu sun gargadi Koriya ta Arewa da ta dakatar da abin da suka kira takula da take yi masu wacce suka ce ba abin da za ta haifar mata illa taimakawa ga rugujewar mulkin kama kayarta.
A cikin wata sanarwa da hukumomin sojan Koriya ta Kudun suka fitar da kuma kakakin hukumar Jeong Joon-Hee ya karanto, sun ce Koriya ta Arewa za ta fuskanci hukunci mai tsanani idan har ba ta dauki wannan kashedi da suka yi mata ba da muhimmanci
Wannan sabuwar sa in sa tsakanin kasashen biyu ta zo ne a daidai lokacin da hukumomin sojan Koriya ta Arewar suka yi barazanar kai hari kan fadar shugaban kasar ta Koriya ta Kudu a matsayin martani ga shirin gudanar da wani atisayen sojoji na hadin guywa da Koriya ta kudun ke shirin gudanarwa da kasar Amirka a watan gobe a matsayin martani ne gwajin makamin nukiliyar da Koriya ta Arewar ta yi a baya-bayan nan.