Kotu a Nijar ta kori batun karan safarar jarirrai
January 30, 2015Cikin mutanan dai, har da tsofon shugaban majalisar dokokin kasar ta Nijar Hama Amadu da aka zargi matarsa da hannu cikin lamarin, da tsofon ministan aikin gona Abdou Labo da shima ake zargin matarsa da wannan batu, wanda shima ya yi kaso na tsawon watanni sakamakon zargin. Kotun birnin Yamai ne dai ta sanar cewa ba za ta saurari wannan kara ba da ya shafi kasashen Nijar da Najeriya da kasar Benin.
Nan take bayan wannan hukunci na kotu, wadanda ake zargi da wannan batu suka barke da sowa tare da nuna farincikinsu kan hukunci na kotu. Masu karan dai suna da kwanaki goma domin daukaka kara muddin dai suna da ja. Kan wannan batu ne dai tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Hama Amadu ya fice daga kasar inda yake gudun hijira a birnin Paris na kasar Faransa.