An hana sanya hijabi a makarantun Indiya
March 15, 2022Talla
Bayan an jima ana cece-kuce kan umarnin gwamnati na hana sanya hijabi a aji, a wannan Talata wata kotu a kasar Indiya ta amince da dokar hana mata musulmi sanya hijabi a makarantu. Kotun da ke jahar Karnataka a Kudancin kasar inda rikicin ya samo asali, ta yanke hukuncin bayan shigar da kara a gabanta ana kalubalantar dokar.
A watan Febrairun da ya gabata, zanga-zangar dalibai mata musulmin ta barke kan batun hana matan sanya hijabi, batun da ya ja hankalin duniya tare da janyo rufe manyan makarantun sakandare da kuma kwalejoji a sakamakon rikicin da ya barke kan haramcin hijabin.