Kotu ta ba da umarni Zakzaky ya ga likitansa
January 22, 2019Talla
Ibrahim Zakzaky da ke zama malamin 'yan kungiyar 'yan uwa Musulmi karkashin kungiyarsu ta IMN, hukumar tsaron farin kayan na rike da shi tun daga watan Disamba na shekarar 2015
An dai kama shi a lokacin da jami'an tsaron Najeriya suka kaddamar da kame-kamen 'yan Shi'a a garin Zariya da ke arewacin Najeriya, inda dakarun suka halaka 'yan Shi'ar 300 kana suka binne su a katon kabari guda.
Lauyan da ke kare Zakzaky Maxwell Kyon, ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa sun nemi kotun ta ba da dama ga likitan da ke duba malamin ya duba shi, saboda rashin kulawar da ta dace da suke gani a hannun jami'an na DSS.