1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta ce dole Jonathan ya gurfana a gabanta

Abdullahi Tanko Bala
October 25, 2017

A  karo na biyu wani alkalin kotu a Abuja ya nemi tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya baiyana a gabansa ko ta halin kaka.

https://p.dw.com/p/2mVB0
Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: picture alliance / dpa

Jonathan din dai yaki halartar wani zaman kotun da aka gudanar da safiyar laraba a Abuja, haka kuma babu wakilcin lauyoyi, duk da umarnin kotun da ta ce yana da shaidar bayarwa a wata shari’ar cin hanci a kasar.

To sai dai ‘yan aiken kotun sun tabbatar da cewar sun kasa mika sammacin ga tsohon shugaban da babu wanda ya san inda yake a yanzu.

Daya daga cikin wadanda ake kara kuma tsohon kakakin jam’iyyar PDP Oliseh Metuh ya nemi shugaban da kuma tsohon mashawarcin tsaron kasar Sambo Dasuki da su bayyana domin bada shaida a bisa zargin halarta tsabar kudi har Naira Miliyan 400 da ke zaman na haramun.

Nigeria Sicherheitsberater Sambo Dasuki
Sambo Dasuki tsohon mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaroHoto: picture-alliance/AP Photo

Tun da farko alkalin kotun mai Shari'a Okon Abang ya rushe wata bukatar kaucewa baiyyana a gaban kotun a bangaren Sambo Dasukin da ake zargi da tura kudin zuwa asusu na kamfanin kakakin .

Alkalin dai yace dole ne Sambo Dasukin ya baiyyana a kotu a ranar 31 ga wannan watan da ke zaman rana ta gaba ta sauraron shari’ar.  Haka kuma ya zama wajibi ga dan aiken kotun da ko dai ya tabbatar da mika sammacin na Jonathan kafin ranar ko kuma ya tabbatar da isar da shi ga tsohon shugaban ta duk wata hanyar da ta dace a cikin shari’a.