Kotu ta dakatar da daina amfani da tsoffin Naira
February 8, 2023Jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka nemi kotun ta tsoma baki tare da haramta wa gwamnatin tarrayar da babban bankin kasar CBN dakatar da amfani da tsoffin takardun kudin Nairar daga ranar Juma'ar nan.
Sai dai wasu alkalan kotun guda Bakwai karkashin mai shari'a John Okoro sun ce sun amince da bukatar ihohin Uku na tsayar da matakin babban bankin na daina karbar tsohon kudin wanda bankin ya tsara zai fara aiki daga ranar 10 ga watan Fabrairu.
Sabon hukuncin dai na nufin karin akalla kwanaki biyar a bangaren kotun kolin da ta tsara sauraron shari'ar a ranar 15 ga watan Fabrairu .
Tuni dai umarnin ya faranta wa bangaren jam'iyyar APC da dan takararta Bola Ahmed Tinubu da ya fitar da sanarwar lale marhabun da umarnin Kotun.
Idris malawgi dai na zaman daya a cikin kakakin yakin neman zaben Tinubun.
To sai dai kuma a yayin da APC ke tsallen murnar nasara, daga dukkan alamu nasarar na zama ta lokaci kankane a cikin umarnin da ke kama da kundin tsarin dokokin kotun a fadar Barrister Buhari Yusuf wani lauya mai zaman kansa a Najeriyar.
Ko ma wane tasiri umarnin kotun koli zai iya yi a takkadamar da ta mamaye kasar a halin yanzu, daga dukkan alamu batun rashin kudin ba zai yi tasiri ga babban zaben da kasar ke shirin gudanarwa ba.
Hukumar zaben kasar INEC ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da zaben kamar yadda aka tsara.
Shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmud Yakubu ya gana da shugaban kasar Muhammadu Buhari da ministocin gwamanti inda ya baiyana cewa ya sami tabbacin hadin kai da nufin tunkarar kalubalen zaben.
Abin jira a gani dai na zaman yadda ta ke shirin kayawa a kotun wadda daga dukkan alamun ke shirin jagorantar lamura cikin fagen siyasar da ke ta kara fuskantar rudani.