1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kotu ta dakatar da gwanjon kayan Nelson Mandela

January 30, 2024

Kayayyakin tarihi akalla saba'in ne na tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Nelson Mandela aka tsara cewa za ayi gwanjonsu a kasuwar birnin New York na Amurka a watan Fabrairu.

https://p.dw.com/p/4bqib
Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela
Tsohon Shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela Hoto: Jon Hrusa/epa/picture alliance/dpa

Hukumar da ke kula da killace kayayyakin tarihi a kasar Afrika ta Kudu ta sanar da dakatar da gwanjon wasu kayayyakin tarihi na tsohon shugaban kasar Nelson Mandela har sai kotu ta yanke hukunci a kan halascin yin hakan.

An dai tsara cewa za a baje hajar Mandelan ta kafar kasuwar Internet karkashin kulawar wani kamfanin New York da ke Amurka, a ranar 24 ga watan Fabarairun da ke tafe tare da hadin gwiwar babbar 'yar marigayin wato Dr Makaziwe Mandela. Marigayi Mandela dai ya kasance shugaba bakar fata na farko kuma jagoran yaki da wariyar launin fata da ya mutu a 2013.

Wannan mataki na gwanjon kayan Nelson Mandela, na shan suka daga al'ummar kasar har ma da gwamnatin kasar da ke goyon bayan shigar da batun kotu da aka yi.

Wasu daga cikin kayayyakin da aka tsara fitar da su domin sayar wa sun hadar da littafin da ya wallafa a gidan yari da fasfo dinsa da kuma bargo da tsohon shugaban Amurka Barrack Obama da mai dakinsa Michelle suka ba shi kyauta.