Kotu ta daure masu zanga-zanga sama da 100 a Masar
May 15, 2016Jami'ai a kasar Masar sun bayyana cewa wasu kotuna guda biyu sun bada hukunci na daurin shekaru biyar ga wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnati 101.
Zanga-zangar da aka yi a watan da ya gabata da ke zama ta kwanciyar hankali a wannan kasa.
Jami'an da ba su son a bayyana sunansu, a ranar Lahadin nan sun bayyana cewa masu zanga-zangar sun karya dokar kasar ta Masar wacce ake ta cece-kuce a kanta tun a shekarar 2013, da ta haramta gudanar da zanga-zanga a titunan kasar.
A kwai kuma wasu masu zanga-zangar 79 da aka ci su tara ta Fam 100,000 wato kimanin Dala 10,000 kowannensu.
Hukuncin dai da ya fita a yammacin ranar Asabar bayan da wata kotu ta yanke hukuncin shekaru biyu a gidan kaso ga wasu masu zanga-zangar 51, saboda su ma sun shiga zanga-zangar ta watan da ya gabata bayan kalubalantar matakin gwamnatin ta Masar na mika wasu tsibirai nata ga mahukuntan Saudiyya.