1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta soke dokar haramta luwaɗi a Yuganda

August 1, 2014

Kotun ta ce lokacin da majalisar dokokin ƙasar ta amince da dokar ba a samu addadin da yakamata ba na 'yan majalisun da suka dace.

https://p.dw.com/p/1CnW2
Jaqueline Kasha
Masu fafutuka na kare hakkokin 'yan luwaɗi a YugandaHoto: DW/S. Schlindwein

Babbar kotun tsarin mulki ta Yuganda, ta yanke hukuncin soke dokar nan wacce ke ƙara tsaurara hukuncin a kan 'yan luwaɗi wacce ta janyo martanin jama'ar ƙasar dama ƙasashen duniya.

Da yake bayyana hukunci soke dokar alƙalin kotun ya ce ba ta da tushe sannan kuma ba ta da makama. Saboda ya ce lokacin da 'yan majalisun dokokin suka amince da ita a cikin watannin huɗun da suka gabata, addadin da yakamata a samu na waɗanda suka kaɗa ƙuri'a bai kai mizanin da ake so ba.

Dokar dai ta tanadi hukuncin ɗaurin rai da rai ga wanɗada aka samu da laifin yin luwaɗin sannan ya zama dole ga jama'a su bayyana 'yan luwaɗin ga hukuma. Tun da fari ƙasashen duniya masu hannu da shuni sun katse wani ɓangare na tallafin da suke bai wa ƙasar ta Yuganda dangane da wanan doka.

Mawalafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar