1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta take umarnin Shugaba Trump kan baki

February 4, 2017

Kamfanin sufurin jiragen sama na Air France ya bayyana a ranar Asabar din nan cewa kofarsa a bude take dan daukar fasinjansa zuwa Amirka wadanda matsalar ta ritsa da su.

https://p.dw.com/p/2WyQb
USA Präsident Trump - Flugzeug
Hoto: Reuters/C. Barria

A Amirka wani alkalin kotun tarayya a birnin Seattle  ya taka birki ga shirin Shugaba Donald Trump na hana baki da matafiya shiga kasarsa daga kasashe bakwai da suka hadar da Iran da Iraki da Yemen da Libiya da Somaliya da Siriya da ke da mafiya rinjaye na al'umma Musulmi.

A wani labarin kuma kimanin mutane 200 ne suka gudanar da wani maci tafe ana raye-raye da kade-kade tun daga katafaren otel din kasa da kasa na Donald Trump zuwa fadar White house da nufin nuna turjiysarsu ga tsare-tsaren na Shugaba Trump makonni kadan bayan kama mulkin Amirka.

Kamfanin sufurin jiragen sama na Air France ya bayyana a ranar Asabar din nan cewa kofarsa a bude take dan daukar fasinjansa zuwa Amirka wadanda matsalar ta ritsa da su, bayan da kotun tarayya ta taka wa Shugaba Trump birki kan umarninsa na hana shigar baki daga wasu kasashe na Musulmi zuwa kasar ta Amirka.

A cewar mai magana da yawun kamfanin na Air France Herve Erschler dukkannin fasinjoji da wannan matsala ta tsaida baki shiga kasar ta Amirka ta shafa yanzu su na da dama muddin suna da takardunsu hadi da Visa.