Kotun Pakistan ta yi da tuhumar tsohon firaminista
November 29, 2023Wata kotu a kasar Pakistan ta yi watsi da laifin da aka samu tsohon Fairaministan kasar Nawaz Sharif na cin hanci, kamar yadda lauyansa ya bayyana. A shekara ta 2018 aka samu Sharif da laifi kan tuhumar cin hanci tare da iyalansa sakamakon wasu gidaje da suka saya a birnin London na Birtaniya, abin da ya saka aka daure shi na tsowon shekaru 10.
Wata babbar kotu da ke birnin Islamabad fadar gwamnatin kasra ta wanke tsohon Firaministan Nawaz Sharif.
A wani labarin kuma tsohon Fiaminista Imran Khan na kasar ta Pakistan da yanzu haka yake daure, ya amince daya daga cikin lauyoyinsa ya tsara wa jam'iyyarsa ta PTI takara na mukamun firaminista zaben da ke tafe, lamarin da ya tabbatar da cewa lauyan Gohar Khan ke zama dan takara kan neman firamnista a jam'iyyar PTI.