Kotun UEMOA ta yi watsi da koken Jamhuriyar Nijar
November 20, 2023Ministan shari'a na kasar ta Nijar ne dai da kanshi ya jagoranci wani taron manema labarai domin ba da haske kan wannan hukunci da ya kira hukunci na ramuwar gayya wanda ba'a yi shi ta hanyar doka a cewar shi ba, ganin cewa baya ma da gwamnatin ta Nijar da ta shigar da kara na gaggawa, akwai kuma wasu kungiyoyi guda bakwai irin cibiyar yan kasauwa ta kasa, kungiyar masu sayar da magunguna, ma'aikatar kula da kayayakin da ke biyowa ta tashar ruwan Cotonou da dai sauransu amma kotun ta yi watsi tare da cewa babu wani abun gaggawa da ta gani a ciki lamarin da Ministan na shari'a Alio Daouda ya ce abin takaici ne.
Karin Bayani: A Jamhuriyar Nijar siyasa ta dauki sabon salo
Shart'ar dai guda biyu ne kasar ta Nijar ta shigar a gaban wannan kotu ciki kuwa har da wannan na gaggawa wanda a cikinsa ne aka bai wa kotun cikokkun bayanai na illolin da takunkumin ke yi wa al'ummar Nijar amma kuma kuma shugaban wannan kotu y ace zabi daya ne kawai hukumomi su mayar da mulki ga inda suka kwace shi idan har suna son dage takunkumi. Sai dai da yake Magana kan wannan batu Mourtala Abdoul Aziz na kungiyar AJPR masu fafutikar kishin Afirka ya ce biyayya ga doka ne ya sa Nijar ta kai wannan kara a gaban wannnan kotu.
Tuni dai a fuskar kungiyar farar hula ta FCR da ba da jimawa ba ta nemi da a saki tsohon shugaban kasa da sauran wadanda aka kama ba bisa ka'ida ba a cewarta ta bakin shugabanta Omar Souley, ya kyautu sojoji da suka karbi mulki su kira duk 'yan siyasa da sauran kungiyoyin kare hakkin jama'a domin samun mafita tunda kotun da ma ECOWAS sun yi tsayin gwamen Jaki.