Kotun Kenya za ta tantance makoman sakamakon zaben Shugaban Kasa
March 30, 2013Talla
A wannan Asabar kotun kolin kasar Kenya ke yanke hukunci game da kalubalantar sakamakon zaben Shugaban kasa da Uhuru Kenyatta ya lashe.
Dan takaran da ya zo na biyu a zaben na ranar hudu ga wannan wata na Maris, Raila Odinga ya yi zargin cewa an tafka magudi na aringizun kuri'u, amma dukkanin mutanen biyu sun yi alkawarin mutunta hukunci na kotu.
Rikicin da ya biyo bayan zaben kasar ta Kenya na karshen shekara ta 2007, ya janyo mutuwan fiye da mutane 1200, tare da jefa tattalin arzikin kasar cikin rudani. Wannan karon 'yan siyasa da 'yan kasar na neman ganin an kaucewa sake maimaita irin wannan rikici.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Halima Balaraba Abbas