SiyasaAfirka
Kotun Senegal ta cire sunan daya daga cikin 'yan takara
February 20, 2024Talla
Kotun tsarin mulkin kasar Senegal ta cire sunan daya daga cikin 'yan takarar shugaban kasa a zaben da aka dage na 25 ga watan Fabarairun nan, bayan wata kwaskwarima da ta yi wa sunayen.
Karin bayani:Rikicin siyasar Senegal
Kotun ta cire sunan Rose Wardini 'yar takara daga kungiyoyin farar hula ba tare da bayyana dalili ba, kuma har yanzu dai ba a sanar da sabon lokacin gudanar da zaben ba, bayan da shugaba Macky Sall ya dage zaben, lamarin da ya haddasa zanga-zangar da ta janyo asarar rayuka.
Karin bayani:Kotun tsarin mulkin Senegal ta soke kudirin dage zabe
To sai dai daga baya kotu tsarin mulkin kasar ta soke wancan mataki na shugaba Sall, har ma ta ba da umarnin hanzarta gudanar da zaben.