Kudancin kasar Sudan na ci gaba da fuskantar hare-hare
April 23, 2018Talla
Rahoton ya kara da cewar cikin hare-hare 750 da 'yan tawaye su ka kai a cikin kankanin lokaci, kayan agaji sun gaza kaiwa ga masu bukata sakamakon hana shige da fice yankunan da ke fama da rikicin da 'yan tawayen suka yi a kasar ta Cibiyar ta zargi bangaren gwamnatin da kuma na 'yan tawayen da konewa tare da sata da mamaye asibitoci da kuma tsare likitoci da ma'aikatan ayyukan agaji a matsayin dabarun yaki.