Kudirin Japan ga MDD a game da Koriya ta arewa
July 10, 2006Japan na cigaba da yin kaimi domin ganin kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya zartar da kudirin sanyawa Koriya ta arewa takunkumi a dangane da gwajin makamai masu linzami da ta yi, hakan nan kuma ta bukaci China ta yi bakin kokarin ta wajen jawo hankalin Pyongyang ta koma teburin shawarwari na kasashe shidda a game da burin ta na makaman nukiliya. Ministan harkokin wajen Japan Taro Aso da takwarar sa ta Amurka Condoleezza Rice sun yi musayar raáyi ta wayar tarho a game da daftarin kudirin, inda suka amince da bukatar sauran kasashe su dauki mataki na bai daya a game da kasar Koriya ta arewa. Kasashen Rasha da China sun baiyana aniyar hawa kujerar na ki a game da daftarin. A halin da ake ciki wata tawagar kasar sin din ta tashi zuwa Pyongyang a yau litinin domin ganawa da mahukuntan kasar a game da batun. A waje guda kuma a yayin da a cikin wannan makon ake shirin gudanar da taron shugabannin kasashe masu cigaban masanaántu na duniya G8 a ana sa ran batun nukiliyar ta koriya ta arewa zata kasance kann gaba a zauren muhawarar.