1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rayuwar masu nakasa a Saliyo

Yusuf Bala/YBMarch 30, 2016

Mutanen da aka sarewa wasu sassa na jikinsu hannu ko kafa na fama da matsaloli na rayuwa a sansaninsu na birnin Freetown na kasar Saliyo.

https://p.dw.com/p/1IMH1
Beinamputierte Fußballmannschaft von Freetown, Sierra Leone
Kwallon kafa tsakanin masu nakasa a SaliyoHoto: Chris Jackson/Getty Images

Fatmata Koromo me kimanin shekaru 18 ta bayyana labarin rayuwarta.

"Ina da shekaru biyu ne lokacin da 'yan tawaye suka sare min hannu a lokacin ne suka kashe mahaifina."


Faith Okrofor Smart, 'yar asalin kasar ce ta Saliyo wacce ke da zama a Birtaniya amma ta sadaukar da rayuwarta dan tallafa wa wadannan mutane da iyalansu karkashin kungiyarta ta Melquosh Charity Mission me tallafin marasa galihu a fannin samar da abinci da kula da lafiya da ma horo na sana'a saboda matsanancin hali na rayuwa da suka tsinci kansu.

Eleanor Abdulai da aka yankewa kafar dama a lokacin yakin na daya daga cikin wadanda suka ci moriyar ayyukan wannan kungiya ta Melquosh inda a yanzu take koyon aiki da na'ura mai kwakwalwa a cibiyar koyar da dabarun shugabanci ta IPAM:

Prozess Charles Taylor Special Court for Sierra Leone
'Yan fafutika a SaliyoHoto: AP

"Kungiyar ta biya min kudin makaranta ta bani na'ura mai kwakwalwa, kungiyar na bani karfin gwiwa a karatun da nake yi, ga tallafin abinci da na lafiya duka ina samu ta hanyar ayyukan wannan kungiya."

Da dama dai cikin wadanda suka sami nakasar a lokacin yakin na Saliyo na fiskantar wariya a cikin al'ummarsu, abin da ya sanya Faith Okrofor Smart da ta kafa wannan cibiya ta Melquosh ta sadaukar da aikinta a Birtaniya dan ta dawo gida ta tallafi wadannan al'umma, wanda a cewarta mahaifinta ma ya sha azaba a hannun 'yan tawaye kafin shekaru biyu daga bisani ya rasu.

Isatu Kaigbo
Yara da ke da nakasa a SaliyoHoto: AP

"Na dawo gida a shekarar 2001 dan na ziyarci mahaifina bayan shekaru 10 a Birtaniya sai dai da na dawo duk na tarar mahaifina ya zube, baya cikin hayyacinsa ya sha duka na 'yan tawaye, sun sumar da shi a daure shi a kan bishiya, an bulbula masa kalanzir da sanya taya a wuyansa kafin daga bisa sojan ECOMOG suna daf da sa masa wuta sojan suka kawo masa dauki."

Irin wahalar da Faith ta gani dai mahaifinta ya sha ta sanya ta ajiye aikinta a Birtaniya ta samu ishashen lokaci dan tallafa wa mutanen da suka sha irin wannan wahala cikin ayyukan jinkai na kungiyarta.

Yakin na Saliyo dai da aka fara a shekarar 1991 ya kwashe shekaru 11 ana yi da ma yin sanadi na halaka sama da mutane 50,000.