1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiya mai tallafawa masu bukatar tabarau a Malawi

December 7, 2016

Wata kungiya mai zaman kanta mai suna One Dollar Glasses mai hadin gwiwa da wata kungiya a kasar Jamus ta dauki aniyar samarwa da masu bukatar tabaran karin gani a kasar Malawi tabaran cikin sauki.

https://p.dw.com/p/2Tv5P
Afrika Ein Dollar Brille
Yarinyar da ta amfana da tabarau na dala daya daga kungiyar One Dollar GlassesHoto: Onedollarglasses/M. Aufmuth

Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta fitar a shekara ta 2014 ne dai, ya nunar da cewa akalla mutune miliyan 150 a fadin duniya na bukatar tabaran karin gani. Bincike ya nuna kusan mutane miliyan daya ne suke bukatar tabarau na karin gani a kasar Malawi, wanda hakan ya haifar da matsaloli ga dalibai a makarantu yadda basu iya cimma burinsu na rayuwa saboda ba sa iya ganin abin da ake koyar dasu akan allo a makaranta, kamar yadda abin yake a bangaren magidanta suma basa iyayin ayyukansu yadda ya kamata har su wadatar da iyalansu duk dai sakamakon raunin idanuwansu. Hakan ce ta sa kungiyar One Dollar Glasses ta dau aniyar magance wannan matsala inda cikin minti 20 zasu yi wa mai bukatar tabaran kara gani tabarau ta hanyar sarrafa karafuna da wani gilashi na musamman akan farashin kudi kasa da Dala guda kacal. Guda daga cikin shugabannin kungiyar a kasar Jamus Alex Armbruster ya ce banda samarwa da mutanen da ke da bukata tabarau, kungiyar na koyar da wannan aiki nata ga marasa ayyukan yi. Masu fama da lalurar ido irin ta rashin ganin abin da yake a nesa ko abin da yake da kankanta suna wahala kafin su samu tabaran karin gani daga gurin likitocin ido. Ya zuwa yanzu dai wannan kungiyar ta One Dollar Glasses na irin wanna aiki a kasashe takwas ciki kuwa har da kasar ta Malawi da Burkina Faso da Benin da kudan cin Amurka da kuma kasar Mexico. A Malawin dai an fi ganin irin wadannan guraren samar da tabarau a kudancin kasar.