1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Afhganistan: IS ta dauki alhaki

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 30, 2018

Kungiyar 'yan ta'addan IS ta dauki alhakin harin ta'addancin da aka kai a ma'aikatar harkokin cikin gida ta Afghanistan da ke Kabul babban birnin kasar.

https://p.dw.com/p/2ycrV
Afghanistan Selbstmordanschlag in Kabul
Harin kunar bakin wake a KabulHoto: Reuters/O. Sobhani

Kungiyar ta sanar da hakan ne ta kafar sadarwa ta Internet ta hanyar kamfanin dillancin labaranta na Amaq, sai dai har kawo yanzu ba ta bayar da wata kwakkwarar shaida da ke nuna cewa ita ke da alhakin kai harin ba. Rahotanni dai sun nunar da cewa mutane sun rasa rayukansu yayin da wasu suka jikkata a lokacin harin. Wani jami'i a ma'aikatar harkokin cikin gidan Afghanistan din, ya sanar da cewa 'yan kunar bakin waken guda uku sun hallaka kansu, an kuma harbe mahari guda. Harin dai na zuwa ne kwana guda bayan da kungiyar 'yan ta'addan Taliban ta sha alwashin kai hare-hare a ma'aikatu da ofisoshin gwamnati dama hukumomin tsaro da ke Kabul din.