1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kungiyar IS ta kaddamar da hare-haren ta'addanci a Kwango

June 8, 2024

Kimanin mutane 60 suka mutu a wani mummunan hari da wani bangare na kungiyar IS ya kaddamar kan fararen hula a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango. Masu ikirarin jihadin sun zafafa hare-haren da suke kaiwa a Kivu.

https://p.dw.com/p/4gop8
Wani tsohon hoton 'yan tawayen M23 dauke da makamai a Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango
Wani tsohon hoton 'yan tawayen M23 dauke da makamai a Jamhuriyar Dimukradiyyar KwangoHoto: Moses Sawasawa/AP Photo/File/picture alliance

A wannan mako kadai kungiyar IS ta halaka fararen hula 29, inda suka yiwa wasu fararen hula kisan gilla a wani kauye da ke kusa da Masau a Kivu, kamar yadda guda daga cikin shugabannin al'umma na yankin Mr. Kambale Gerve, ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na dpa.

Karin bayani: Kwango: Sabon rikici a arewacin Kivu 

Hukumar bada agajin gaggawa ta Red Cross ta ce sun yi nasarar kwaso gawarwaki 60 daga yankin, yayinda da wasu kuma ke can a warwatse akan tituna, kasancewar yankin na da hadarin shiga.

Karin bayani:  Kwango: Fada ya barke a Arewacin Kivu

Gerve, ya kuma kara da cewa "yan tawayen Allied Democratic Forces (ADF) na kasar Uganda da suka kulla kawance da kungiyar IS a 2019, sune suka kai harin na ta'addanci.