1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagerun IS sun kai hari Afghanistan

Lateefa Mustapha Ja'afar SB
July 22, 2018

Mataimakin shugaban kasar Afghanistan Abdul Rashid Dostum ya tsallake rijiya da baya na wani harin tsagerun kungiyar IS masu kaifin kishin addinin Islama.

https://p.dw.com/p/31tJL
Afghanistan Kabul Vizepräsident Abdul Raschid Dostum
Hoto: REUTERS

Kungiyar IS ta sanar da cewa ita ke da alhakin wani harin kunar bakin wake da aka yi nufin kai wa a kan mataimakin shugaban kasar Afghanistan Abdul Rashid Dostum.

Kamfanin dillancin labarai na Amaq da ke yada farfagandar kungiyar ta IS ya bayyana cewa dan kunar bakin wake ya tayar da bam a cikin dandazon jama'ar da ta yi dafifi domin tarbar mataimakin shugaban kasar ta Afghanistan, da ya dawo gida bayan kwashe tsahon sama da shekara guda yana samun mafakar siyasa a Turkiya bisa zarginsa da gallaza wa tare da cin zarafin abokin hamayya na siyasa.

Shi dai Dostum ya tsallake rijiya da baya, a harin da aka nufi kai masa a kusa da filin jiragen sama na Kabul babban birnin kasar. Kawo yanzu babu karin bayani dangane da adadin wadanda harin ya rutsa da su.