NATO ta fara ficewa daga Afganistan
April 29, 2021Talla
Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da shugaban Amirka Joe Biden ya sanar da aniyarsa ta janye dakarun kasarsa daga kasar Afganistan kuma ya yi nasarar shawo kan sauran kasashen da ke taimakawa a yakin da ake yi da 'yan Taliban da su ma su fice.
Sanarwar ta kara da cewar duk wani yunkuri na hari daga mayakan na Taliban a wannan lokacin zai gami da fushin kungiyar. Ana sa ran kammala janye dakaru a cikin 'yan watanni masu zuwa nan gaba.
A yayin da su kuma Amirka za su fara na su a watan Satumbar shekarar nan, watan da kasar ke cika shekaru 20 da kaddamar da yaki a Afganistan tun bayan harin 11 ga watan Satumban 2001 da ake wa lakabi da 9/11, da ya hallaka daruruwan mutane a Amirka.