Kura ta lafa a gidan yarin Yaounde
July 24, 2019Fursunonin sun nuna cewar suna cikin wani hali maras kyau na rashin samun abinci da rashin kula ta fanin kiwon lafiya. Jamian tsaro sun yi amfani da kulake da barkonon tsofuwa domin tarwatsa gangamin fursunoni tare da hanasu arcewa daga cikin gidan kurkukun. Tun da farko fursunonin ‘yan Ambazoniya sun kankane hanyoyin shiga gidan kason suka hana shige da fici tare da raira taken yankin na Ambazoniya
Wani dan siyasar marubu na kasar Kamaru Enoh Meyomesse da ke yin hijira a wanda kafin ya zo Jamus shekaru uku da suka wuce aka tare shi a gidan kurkun na Kodengui ya ce akwai cinkoso mai yawa a gidan kason. Ya ce gidan kason na Kodengui a gina shi domin daukar fursunoni 800 amma a yau akwai ’yan kaso kusan 5000 a ciki. Yanzu haka dai a kasar ta Kamaru ana tsare da ‘yan siyasa da dama masu ra’ayin balewa.
Wannan ba shi ne karon farko ba da ake samun bore a gidajen fursuna na Kamaru kasar da ke cikin wani hali na tashin hakali kusan shekaru uku a yankin da gwanatin take yi da masu neman balewa ‘yan yankin dake magana da harshen inglishi wanda kawo yanzu yakin ya yi sandiyyar mutuwar dubban rayukan jama‘a tare da tilastawa wasu dubbai ficewa daga matsugunasu