Kurdawan Iraki sun bukaci da a ba su makaman zamani
September 25, 2014Talla
Kurdawa a Iraki sun bukaci gamaiyar kasa da kasa ta ba su karin makamai kuma na zamani a yakin da suke yi da 'yan ta'addan kungiyar IS da ke fafatukar kafa daular Musulunci. Bayan wata tattaunawa da ya yi da ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen wadda a wannan Alhamis ta kai ziyarar ba-zata arewacin Iraki, shugaban Kurdawa Massud Barzani ya ce matukar mayakan Kurdawa na Peshmerga suka samu wadannan makamai na zamani, to ba bu wata bukatar neman karin tallafi a yakin da suke yi da 'yan IS. Ba da jimawa ba ne dai ayarin farko na makaman da Jamus ta alkawarta wa Kurdawan, za su isa yankin. Sannan sojojin rundunar Jamus za su horas da mayakan Kurdawan yadda za su sarrafa wadannan makamai.