Indiya: Kuri'ar yankan kauna ga Modi
August 10, 2023Talla
Jam'iyyun adawar kasar ne dai suka gabatar da kudurin kada kuri'ar yankan kaunar ga Firaminista Narendra Modi bayan kiraye-kiraye ga gwamnatinsa, a kan zubar da jini a yankin Arewa maso Gabashin jihar Manipur da ke barazanar fuskantar yakin basasa. Sai dai ana zargin firaministan ya yi gum da bakinsa kan rikicin da ya barke a yankin, tun a watan Mayun wannan shekarar. Ana dai ganin kudurin kada kuri'ar ba zai yi wata barazana ga gwamnatin Modi ba, sakamakon gwamnatin hadakarsa na da kujeru 331 a majalisar wakilai.