1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwalejin farko ta dalibai makafi a Indiya

June 22, 2012

Shirin bada ilimi mai zurfi domin baiwa nakasassu damar cin moriyar rayuwarsu a tsakanin al'umma

https://p.dw.com/p/15Jk0
Hoto: DW

A kasar Indiya, hukumomi a lardin Kerala, sun bude wani kwaleji, wanda shine na farko, musamman domin bunkasa karatun dalibai makafi. Daya daga cikin su shine Sujesh, dan shekaru 11, wanda yace burin sa, idan ya girma, kuma ya kare karatun sa a kwalejin na makafi a Kerala, shine ya zama darektan fina-finai. Sujesh yace har ma yana da shirin daukar duk tsawon lokacin sa na hutu domin rubuta wani wasan kwaikwayo da ake iya maida shi fim. Hukumomi a lardin sun zama jagora a game da bude wannan makaranta, wadda ta kwana ce ga dalibai dake bukatar horo na musaamman saboda nakasar su ta makanta. Johnson Joseph, wanda shine shugaban makarantar, yayi na'am da burin da Sujesh ya sanya a gaban sa. Yace "muna bukatar dalibanmu su zama masu zaman kansu, su rika tunani na kansu", kuma ya nunar da cewar makafi misalin miliyan 40 ake dasu a duiya baki daya, inda miliyan 12 daga cikin su suke zaune a Indiya.

Makarantar dai an kafa ta ne a shekara ta 1962, tare da taimakon kungiyoyin agaji, to amma a yanzu gwamnatin Kerala ce take biyan albashin malamai da kayan sanyawa na yan makarantar. A dakinsa, Sujesh yana da Computer, wato na'ura mai kwakwalwa. A duk lokacin da yake aiki kanta, na'urar zata rika amsa umurni, ko bashi umurni ta amfani da murya, maimakon ya karanta. Na'urar takan ce yayi "dama" ko yayi "hagu", takan kuma sanar dashi abin dake gudana idan ya amsa wannan umurni. Fasahar da Sujesh yake amfani da ita cikin harshen Ingilishi da aka kirkiro a Amirka, ana sa ran shekara mai zuwa za'a kaddamar da ita karon farko cikin harshen Malayalam, wanda shine babban harshen mazauna lardin Kerala, kamar yadda wani malami ya baiyana.

Da aka tambayesu, me suke da burin yi, idan suka kare karatun su a kwalejin na makafi, wasu 'yan mata guda biyu dake kusa suna sauraron wakoki cikin karshen Malayalam a dandalin Youtube, daya daga cikin su tace, "burina shine in zama malama mai koyar da ilimin fasaha". Tace zata ci gaba da neman ilimi har sai ta kai ga shiga jami'a, watakila a jihar Tamil Nadu dake makwabtaka da Kerala, ko da shike tana sane da cewar samun nasarar cimma wannan buri nata ba zai zama abu mai sauki ba. Duk da haka, tare da karfin zuciya tace," a shirye nake in fuskanci wannan kalubale". Watakila ma dalibar ta sami sa'ar ci gaba da zama a garin Aluva, inda kwalejin na makamafi yake. Shi dai wannan gari bashi da nisa da wani babban gari mai suna Cochin, dake jan hankalin yan yawon bude ido masu yawa dake zuwa daga jiragen ruwan yawon shakatawa, domin nuna sha'awarsu ga gine-gine na tarihi na tun zamanin turawan Portugal.

Indien Kerala Jason Balaman Blindenschule
Jason Balaman malami a makarantar KeralaHoto: DW

Johnson Joseph shugaban makarantar ta makafi tare a farin ciki yace, "muna nan muna aikin gina kwalejin makafi." Makarantar zata kasance ita ce ta farko ta makafi a Indiya, kuma tun daga watan Satumba na wannan shekara, dalibai zasu fara karatun samun digiri. Yayin da da dama daga cikin daliban sa sukan sami damar wucewa zuwa wasu jami'oi domin koyon ilimi mai zurfi a fannin aikin injiniya ko zama likitoci, amma daliban sukan yi fama da wahaloli da matsaloli, tun da shike har yanzu jami'oin ba'a yi masu tanadi sosai na yadda zasu kula da bukatun dalibai masu nakasa ba.

To sai dai duk da wannan karfin zuciya da ya nuna, Johnson Joseph ya yarda da gaskiyar cewar masu daukar ma'aikata da dama sukan nuna kyamar su ga daukar makafi aiki. A ra'ayin sa, kamata yayi gwmanati ta bullo da wani shiri inda za'a tilastawa kamfanoni da masu daukar aiki su rika daukar masu nakasa a ma'aikatun su, kamar dai yadda ake aiki da tsarin nan da ya tilasta daukar yan kabilu marasa galihu a kasar ta Indiya. Daliban sa, injishi, ya kamata su rika samun aiki a kasar dake ci gaba da bunkasa, kuma ware masu wani adadi a ko wace ma'aikata ne kadai zai tabbatar da hakan. Wani malami a makarantar ta makafi, Jason Balaman yayi tambayar: "Wane dalili masu daukar aiki suke dashi na daukar makafi, idan har zasu iya daukar masu idanu?" Balaman, tsohon injiniyan gine-gine, wanda shi kansa makaho ne, yace a lokacin da ya rasa idanunsa, sai da yayi shekaru biyu a cikin gidan iyayen sa, bai fita ko ina ba. Yace, "naji kunyar fita daga cikin gidan, saboda ban san abin da makwabta zasu rika fadi ba." Jason yayi bayanin cewar lokacin da ya rasa idanun sa, ya nemi ayi masa aiki, amma abin ya zama da tsadar gaske. Gwamnati da kungiyoyi agaji na cikin gida da na kasa da kasa dake aiki a Kerala suka ki biyan kudi ko daukar nauyin aikin da zai ceto idanun nashi. Daga baya yace yaji cewar wai da kudin da za'a kashe domin yi masa aiki shi kadai, ana iya yiwa masu ciwon idanu da yawan gaske aiki. Sai da Jason da ya dauki shekaru biyu kafin ya daidaita rayuwar sa da halin da ya shiga na makanta. A bara yayi aure, kuma yace ko da shike yana farin cikin samun damar koyar da dalibai kamar Sujesh, amma har yanzu rayuwarsa tana cikin wani yanayi mai wahala.

Kerala Blind School
Sujesh a makarantar makafi ta KeralaHoto: DW

Mawallafi: Baig/Umaru Aliyu
Edita: Zainab Mohammed