Kwamtin Sulhu yayi kira ga Koriya Ta Arewa da ta yi watsi da gwajin makamin nukiliya
October 7, 2006Talla
Ba tare da wata hamaiya kwamitin sulhun MDD yayi kira ga KTA da ta yi watsi da shirin ta na gudanar da gwajin makaman nukiliya na farko a cikin kasar. Japan ta nunar da cewa KTA ka iya gudanar da wannan gwaji watakila a karshen wannan mako. Shi kuwa jakadan Amirka a MDD John Bolton cewa yayi Amirka na matsa kaimi don samar da wata sahihiyyar hanyar da za´a tinkari abin da gwamnati a Washington ta kira tsokana daga KTA. A tsakiyar wannan mako gwamnati a birnin Pyongyang ta ba da sanarwa cewa tana shirye shiryen gudanar da gwajin makamin nukiliya, wanda ta ce yana da muhimmanci a kokarin dakile barazana ta soji da tattalin arziki daga Amirka. Wata majiyar kasar Sin ta rawaito cewa KTA na shirin gwajin wani makamin nukiliya a wani wuri mai zurfin mita dubu 2 a karkashin wani tsohon ramin hakan kwal.