1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwango: Kotu ta yanke wa sojoji 25 hukuncin kisa

July 4, 2024

Wata kotu da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta yanke wa sojojin kasar kimanin 25 hukuncin kisa kan zarginsu da tsrerewa daga fagen daga a fafatawar da ake yi da 'yan tawayen M23.

https://p.dw.com/p/4hqVM
Demokratische Republik Kongo Gericht Symbolbild
Hoto: Pond5/IMAGO

A jimilce dai mutane 31 ne da suka hadar da mata fararen hula guda hudu da sojoji 27 aka gufarnar a yayin zaman wuni guda da kotun hukunta sojoji ta Butembo mai mazauni a arewacin Kivu ta yi a ranar Laraba 03.07.2024.

Karin bayani: Zaman shari'a kan yunkurin jyuin mulki a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Guda daga cikin lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhuma Barista Jules Muvweko ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP aniyarsu ta daukaka kara kan hukunci kisan da ya shafi kyaftin biyu, duk da cewa an wanke sauran daga laifin saboda rashin cikakkun hujjoji.

Karin bayani: Kwango: M23 ta karbe iko da mahakar ma'adinai ta Rubaya

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan tawayen M23 masu samun goyon bayan Ruwanda ke matsa lamba, lamarin da ya kai su ga karbe iko da yankuna da dama na arewacin Kwango.