An sami rabuwar kawuna bayan kawo karshen kawance
December 7, 2020Shawarar da Shugaban Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango Felix Tshisekedi ya yanke na kawo karshen kawancen da ke mulkin kasar tun tsawon shekaru biyu ta raba kawunan al'ummar kasar. Shi dai shugaban ya shafe wata guda yana tuntubar bangarori da dama kafin ya raba gari da jam'iyyar FCC ta tsohon shugaba Joseph Kabila saboda ba ta ba shi damar yin aiki yadda ya kamata. Shugaba Tshisekedi ya nemi jerawa da wanda ya gada a kujerar mulki wato Joesph Kabila bayan zaben shugaban kasar Kwango na 2018, sakamakon rashin samun yawan 'yan majalisa da za su ba shi damar taka rawar gaban hantsi. Saboda haka ne bangarorin biyu suka hada gwiwa domin gudanar da harkokin mulki tare, kasancewar mafi rinjayen 'yan majalisa da aka zaba sun fito ne daga FCC ta tsohon shugaban Joseph Kabila. Karin bayani: Kamun ludayin shugaba Felix Tshisekedi
Amma rashin fahimta da aka fuskanta tsakanin sassa biyu kan alkiblar da ya kamata gwamnati ta fuskanta ya sa Shugaba Tshisekedi raba gari da Kabila. Hasali ma jawabin da ya yi ranar Lahadi, wanda aka dade ana jira, ya sa magoya bayan Tshisekedi fitowa kan tituna don nuna murnar kawo karshen kawancen FCC-CACH.Wasu mazauna Kinshasa babban birnin Kwango sun goyi bayan kawo karshen kawancen gwamnatin, inda suka yi imanin cewa yanzu shugaban kasar ya samar wa jam'iyyarsa 'yanci kuma zai iya inganta yanayin rayuwar' yan Kwango. Shugaba Felix Tshisekedi ya sanar cewa zai nada wani babban jami'i da za a dora wa nauyin zawarcin wasu jam'iyyu da ke da wakilci a majalisar dokokin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango da nufin kulla sabon kawancen da zai ba su damar samun rinjaye. Karin bayani: A cimma matsayar kafa gwamnati a Kwango
Ma'ana yana neman jam'iyyar da ba za ta kawo masa tarnaki imma a majalisa ne koko a harkokinsa na mulki ba. Sai dai wasu 'yan Kwango na ganin cewa Shugaba Tshisekedi ya yanke shawara cikin sauri, lamarin da ka iya jefa kasar ta Kwango cikin rudani, kuma ya sa shi gaza sauke alkawuran ci gaba da ya yi alkawari. Hadin gwiwar jam'iyyun adawa na Lamuka karkashin jagorancin Martin Fayulu ya ki ce uffan game da rikicin siyasa da gwamnati ta samu kanta a ciki, yana mai cewa ba abin da za su ce a kan abin da suka kira barayi biyu da ke fada kan dukiyar da suka sata.