Kwankaso: A guji tayar da hankali a Kano
March 15, 2019Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda shi ne jigo a jam'iyyar ta PDP a jihar ta Kano ya tabo batutuwa da dama a hira ta musamman a kan zaben na gwamnan jihar Kano da ma wasu jihohi biyar na Najeriya, inda hukumar zaben za ta sake maimaita zabe a wasu yankuna domin tantance wanda ya samu nasara. Ya ce bukatarsu ita ce a yi zaben cikin kwanciyar hankali domin yi wa kowa adalci, domin akasin haka ba zai yi wa kowa dadi ba a daukacin tsarin dimukuradiyyar Najeriyar.
Tun kafin wannan dai, ana ta kokarin ganin an gudanar da wannan zabe da za’a sake a jihohi shida na Najeriya cikin kwanciyar hankali, inda hukumar zaben kanta ta bayyana dalilai da suka sanya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba. Abin da ya sanya Barrister Mainasara Umar mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum ya bayyana bukatar kamanta adalci.
Zargin tafka magudi na kara amo sosai a tsakanin manyan jam'iyyu biyu na PDP da APC a kusan dukkanin jihohin da ake fuskantar wannan batu na maimaita zabe a wasu sassa a jihar ta Kano. Abin da ya kara daukan hankalin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, jigo a jamiyyar PDP, bisa sakamakon da aka sanar cewa tana kan gaba a zaben jihar .
A yayin da hankali jama’a ya dauku zuwa ga jihohin shida da za’a sake maimaita zaben gwamnonin wato Kano, Sokoto, Adamawa, Bauchi, Plateau da Benue, nauyi ya koma kan hukumar zaben na tabbatar da kamanta adalci ta yadda za’a wanye lafiya.