Kwashe daruruwan 'yan tawayen Siriya daga Homs
May 7, 2014Daruruwan 'yan tawayen Siriya sun janye daga tungarsu ta karshe da ke tsakiyar birnin Homs, yankin da ya kasance cibiyar boren adawa da shugaba Bashar al-Assad. Wannan na zama wata nasara ga shugaban makonni kalilan kafin zaben kasar da bisa ga dukkan alamu zai sake lashewa. Ayari biyu na motocin bas-bas sun fice daga birnin da yaki ya daidaita, dauke da mayakan 'yan tawaye zuwa wani tudun mun tsira da ke hannun 'yan tawaye da ke wajen birnin. Hakan dai ya biyo bayan wata yarjejeniya da aka cimma tsakanin masu ta da kayar bayan da dakarun da ke biyayya ga shugaba Assad. A daidai lokacin da suke barin birnin na Homs, an sako firsinoni da ke hannun 'yan tawaye a biranen Aleppo da Latakia, duk a karkashin yarjejeniyar.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman