1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin Labarin Wasanni

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
September 14, 2020

Borussia Mönchengladbach da Bayer Leverkusen sun fara gasar kalubalen neman lashe kofin kwallon kafar Jamus da kafar dama. Akwai saran karin wasanni.

https://p.dw.com/p/3iS03
DFB Pokal Finale I Bayer Leverkusen I Bayern
Bayern Munich ce ta lashe kofin kalubale na banaHoto: Getty Images/AFP/R. Wittek

A daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan a fara kakar Bundesliga wato babban lig din kwallon kafar Jamus, kungiyoyin kasar sun kara da junansu a karshen mako a wasan farko na zagayen farko na gasar neman lashe kofin kalubale na Jamus din a bana. Daukacin kungiyoyin da ke bugawa a babban lig din Jamus ba su fuskanci matsala wajen zuwa zagaye na gaba ba. Hasali ma Borussia Mönchengladbach ta kasance wacce ta fi burgewa, inda ta ci kwallaye takwas a gaban FC Oberneuland da ke wasa a rukuni na hudu na lig din Jamus. Ita kuwa Bayer Leverkusen wacce ta buga wasan karshe a kakar wasan da ta gabata, ta yi wa FC Eintracht Norderstedt dukan kawo wuka da ci bakwai da nema. Haka ita ma FC Augsburg da irin wannan sakamako na bakwai da babu ta doke Eintracht Celle.

A nata bangare kuwa RB Leipzig ta doke FC Nuremberg da ci uku da nema, yayin da Eintract Frankfurt da Stuttgart suka sha da kyar a kan Munich 1860 da ci biyu da daya da Hansa Rostock da ci daya mai ban haushi. A zahirin dai, Hertha Berlin ce kawai ta fadi ba nauyi yayin wannan zagayen farko, inda kungiyar babban birnin Jamus ta tashi da hudu yayin da abokiyar hamyyarta Eintracht Brunswick ta lallasata da ci biyar. Sai dai manyan dawa na fagen kwallon kafar Jamus Bayern Munich da Borussia Dortmund ba su fara wasa ba tukuna. A watan Oktoba ne yaya babban ta Muncih, za ta shiga a dama d ta kece raini a wannan Litinin da makwabciyarta ta Duisburg, lamarin da ke zama zakaran gwajin dafi na burin da Borussia Dortmund din ta sa a gaba na nasarar lashe wannan kofi a wannan karo, a cewar Lucien Favre mai horas da kungiyar ta Dortmund: "A bayyane yake cewa dole ne - ko kuma, ina so in ce muna son lashe kofin kalubale na Jamus."

Bundesliga FC Augsburg v Borussia Dortmund
MAi horas da 'yan wasan kwallon kafa na kungiyar Borussia Dortmund, Lucien FavreHoto: Getty Images/Bongarts/S. Widmann

Yanzu kuma sai mu nufin Ingila, inda aka koma fagen daga na Premier League bayan hutun bazara. Labarin da ya fi daukar hankali a wannan lig da ya fi samun karbuwa a duniya, shi ne nasarar da Everton ta samu a kan Tottenham da ci daya da nema, bayan da ta bita har gida. Wannan dai shi ne karon karfo cikin shekaru takwas da Everton ta nuna irin wannan bajinta a kan dodonta Totenhem. Ita ma Leiceste ta fara da kafar dama inda ta lallasa West Bromwich Albionda ci uku da nema. Ita kuwa Liverpool da ke zama zakaran kwallon Ingilar, ta yi nasara da ci hudu da uku a kan 'yar auta Leeds da ta haura babban lig a bana.

Godiya ta tabbata ga Mohamed Salah na Masar wanda ya zura uku daga cikin kwallayen hudu. Wannan ya bai wa Salah damar kafa tarihi a Liverpool na zama dan wasan da yake zura kwallo a ranar farko, tun bayan da ya shiga kungiyar shekaru hudu ke nan da suka gabata, kuma wanda ya fi ci mata kwallo a ranar farko tun shekaru 32 da suka wuce. A sauran wasannin kuwa Arsenal ta doke Fulham da ci uku da nema, yayin da Newcastle ta samu nasara a West Ham da ci biyu da nema, ita kuwa Southhampton ta yi wa Crystal Palace ci daya mai ban haushi.

A Faransa kuwa Olympique Marseille ta yi abin kai, inda a karon farko cikin shekaru tara ta samu nasara a kan abokiyar gabarta Paris Saint Germain da ci daya mai ban haushi.

A Najeriya, bayan kwashe watanni na haramci da ma dakatar da harkokin wasan kwallon kafa a kasar saboda hana yaduwar cutar COVID-19, kasar ta kama hanyar sake bude wasanin kwallon kafa na rukuni-rukuni, abin da ya sanya ma'aikatar wasani bukatar fitar da sahihin tsari na tabbatar da yadda za a gudanar da wasannin ba tare da matsala ba, shigen yadda suka gudana a kasashen da kwallo ya fi karbuwa kamar Ingila da Jamus, inda ake gudanar da wasanni ba tare da 'yan kallo ba, kuma bisa tsauraran tsrain kiwon lafiya.

Schweiz Zürich FIFA Logo am Hauptquartier
Zargin cin hanci a hukumar kwallon kafa ta duniya FIFAHoto: picture-alliance/dpa/S. Schmidt

Wata kotu a kasar Switzerland ta fara sauraran bahasi daga tsofaffin manyan jami'an FIFA da ake zargi da hannu, wajen badakalar karkarta kudin hakkin mallaka na kafafen talabijin. Bincike mai zurfi aka gudanar na tsawon shekaru, kafin kotu ta gayyaci Jerome Valcke tsohon mataimakin shugaban FIFA da Nasser Al-Khelaifi na kungiyar PSG da kafar sadarwa ta BeiIn Media. Ko da shike  an dade ana jiran wannan shari'ar, amma ta zo a daidai lokacin da annobar corona ta sa a lokacin bazara aka kasa gano gaskiya a kan zargin cin hanci da rashawar, wajen danka kofin Duniya na 2006, sannan kuma bincike da kotu ke yi kan haɗa baki da masu shigar da kara da jami'an FIFA suka yi da wasu alkalan Switzerland, ya sa ana shakku kan sahihanci hukuncin da kotun za ta yanke.

A fagen tennis, Dominic Thiem dan kasar Ostiriya ya cire wa kansa kitse a wuta a US Open, inda ya lashe kofinsa na farko na Grand Slam, bayan da ya doke Bajumashe Alaxander Zverev cikin sa'o'i hudu da minti daya. Abin mamakin ma dai shi Bajamushe Zverev ya fara lashe mataki biyu na wasan, kafin reshe ya juye da mujiya, lamarin da ya sa Thiem samun nasara a mataki na biyar. Sai dai duk da bakin cikin rashin samun nasara da Alexander Zverev ya nuna, amma yayi alkawarin kara kaimi domin lashe muhimmiyar gasar tennis nan gaba.

A rukunin mata kuwa, 'yar Japan Naomi Osaka ta lashe gasar Grand Slam din karo na uku bayan da ta doke tsohuwar lamba daya ta duniya 'yar Belarus Victoria Azarenka da ci daya da shida, shida da uku, shida da uku. Amma kuma baya ga nasarar da ta samu, jajircewar da ta yi wajen yaki da nuna wa bakar fata wariya karkashin shirin nan na "Black Lives Matter" ne ya sanyata a  kanun labarun jaridun Amirka, saboda a kowanne wasa, Naomi Osaka wacce mahaifinta dan Haiti ne amma ta tashi a Amirka, tana shiga fagen wasa da kyallen rufe baki da hanci don karrama bakaken fata da 'yan sanda suka yi ajalinsu sakamakon amfani da karfi. Daidai da a kasarta ta haihuwa Japan, an yaba da kwazon gwarzuwar ta tennis.