1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni 26.06.2023

Mouhamadou Awal Balarabe
June 26, 2023

Hukumar kwallon kafar Afirka ta yi barazanar dakatar da kungiyoyin Najeriya daga gasar zakaru idan ba su samar da rukunin mata ba. Maroko da Ghana sun kai bantensu a wasan farko na neman lashe kofi.

https://p.dw.com/p/4T57Q
Logo CAF  - Confédération Africaine de Football

Maroko da Ghana sun kai bantensu a wasan farko na neman lashe kofin Afrika na kwallon kafa na 'yan kasa da shekaru 23 da haihuwa da ke gudana a Maroko, bayan da suka doke Guinea da ci 2-1 da kuma Kwango da ci 3-2. Ita kuwa Mali kuwa ta mamaye Gabon da 3-1,  Nijar ta ba wa marada kunya ta hanyar nuna wa Masar turjiya tare da tashi wasa 0-0. Ita dai Masar da ke rike da kofin ta baras da kyawawan hare-hare da ta ci gajiya, inda ta buga su a kan turken mai tsaron gida, ba tare da Nijar ta nemi taka rawar gani ba. Baya ma ga samar da ja gaban 'yan kasa da sherkaru 23 na Afirka, gasar za ta samar da gurabe uku na kasashen da za su cancanci shiga gasar Olympics ta Paris a shekara ta 2024.

Ingila ta tsallake zuwa zagaye na gaba na gasar 'yan kasa da shekaru 21 da haihuwa ta Turai da ke gudana a Georgia da Romaniya, bayan nasarar da ta samu a kan Isra'ila  da ci 2-0. Su ma Spain da Ukraine sun samu tikitin zuwa wasan kusa da na karshe na wannan gasa, yayin da Faransa da ta doke Norway  da ci 1-0 ta fara tsammanin hayewa zagaye na gaba saboda ita ce kan gaba a rukuninta.

Italiya ta samu nasara a kan Switzerland da ci 3-2. Amma dai Jamus da ke rike da kofin 'yan kasa da shekaru 21 na Turai ta ci gaba da nutsewa sakamakon shan kashi a hannun Jamhuriyar Czech da ci 1-2. Idan dai tana son ganin badi, to dole ne Mannschaft dole ta yi nasara ko ta halin kaka a kan Ingila a wasanta na gaba kuma ta yi fatan Isra’ila ta samu sakamako mai kyau, ma'ana nasara ko kuma kunnen doki, ko kuuma a doke Jamhuriyar Chek ta barasa da wasanta.

A ci gaba da hada-hadar musaya da saye da sayar da 'yan wasa da manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya ke yi, FC Barcelona ta kulla yarjejeniya da Ilkay Gündogan kyaftin din Manchester City dan kasar Jamus ya har zuwa shekarar 2025. Cikin sanarwa da kungiyar ta Catalonia ta fitar ta ce Euro miliyan 400 ta biya kafin a mika mata dan wasan na tsakiya da ya lashe gasar zakarun Turai na baya-bayan nan.

Fussball l Gündoğan wechselt zum FC Barcelona
Hoto: DAniel Roland/AFP

A nata bangaren Manchester City tana ci gaba da zawarcin  dan wasan RB Leipzig Josko Gvardiol dan asalin Croatia, inda ta yi tayin biyan miliyan 77 na fan. Dama City tana nuna maitarta a fili a game da dan wasan Paris St-Germain Achraf Hakimi komai tsadanta kudin da za a yi.

Ita kuwa Kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya na son sayen karin manyan ‘yan wasa, inda na baya-bayan nan da ta nema ya kasance Demarai Gray dan Jamaica da ke buga kwallo a Everton. Dama dai takwarata ta Al-Itihad ta kasar Saudiyya ta sayi manyan 'yan wasa da dama ciki har da Ngolo Kanté da Karim Benzema na Real Madrid.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF ta bai wa NFF da kungiyon kwallon kafa na Najeriya wadanda za su fafata a gasar Champions League da Confederation wa'adin  talatin ga wannan wata Yuni don su samar da kungiyoyin mata ko kuma ta haramta musu shiga halartar dukkanin gasar. To ko wasu matakai Najeriya ke dauka a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan wa'adin ya cika?

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani