Lashe kofin zakarun Afirka al-Ahly ta kafa tarihi
July 19, 2021Wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Afirka ya gudana a ranar Asabar da ta gabata, inda aka fafata tsakanin al-Ahly ta Masar da Kaizer Chiefs ta Afirka ta Kudu. Kuma a karo na 10 a tarihinta, kungiyar ta Alkahiran Masar ce ta daga kofin sakamakon doke 'yan Afirka ta Kudu na Kaizer Chiefs da ci 3-0 da ta yi, wanda hakan ke kara tabbatar da babakerenta a fagen tamaular wannan nahiya.
Wannan shi ne karo na uku a tarihi da al-Ahly ta samu nasarar daukar kofin zakarun Afirka a jere, lamarin da ya sa ta yi wa babbar abokin hamayyarta ta Zamalek mai kofuna biyar zarra. Godiya ta tabbata ga kocin kungiyar ta Masar Pitso Mosimane, dan asalin Afirka ta Kudu, wanda karkashin horaswarsa Alhy ta lashe kofin zakarun Afirka sau uku a rayuwarsa. Hasali ma a yanzu shi ne kocin Afirka da ya fi daukar kofin zakarun Afirka cikin tarihi. Saboda haka ne ya yi kira ga kungiyoyin kasashen Afirka da su yawaita amfani da masu horaswa na gida maimakon na kasashen Turai.
"Mu ’yan Afirka, za mu iya cimma nasara da kanmu. Me ya sa bamu kara yarda da kanmu? Aljeriya ce ta lashe kofin kasashen Afirka kuma kociyanta dan Aljeriya ne, ko ba haka ba ne? Kuma a wasan karshe, Aliou Cissé, dan kasar Senegal ne ya jagoranci tawagar Senegal. Muna matikar daraja masu horar na Turai. Har yanzu muna neman koci daga Turai domin ba shi damar tafiyar da kungiya, alhali muna da kwararru." Sakamakon lashe wannan kofi da al-Ahly ta yi, za ta wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniya ta kungiyoyin da suka zama zakarun nahiyoyin wanda za a buga a Japan a watan Disamba mai zuwa, lamarin da ya dadada ran magoya baya da shugabannin kwallon kafa a Masar, kamar yadda za ku ji cikin wannan rahoton da wakilinmu Mahmud Yaya Azare ya aiko mana da Alkahira.
Senegal ta sha kashi a gasar COSAFA
A wasan karshe na cin Kofin COSAFA ta yankin gabashin Afirka a bugun fenariti Senegal ta sha kashi a hannun Afirka ta Kudu da ci 4-5, a filin wasa na Nelson Mandela Bay da ke Port Elizabeth. Dama dai kasar Senegal ta kasance bakuwa ta musamman da aka gayyata kamar yadda aka saba domin halartar gasar COSAFA. Sai dai yawancinsu 'yan Senegal suna wasa ne a rukuni na biyu ko na uku na kulob dabam-dabam. A nata bangaren kungiyar kwlalon kafar Afirka Afirka ta Kudu ta kammala gasar COSAFA ba tare da an zira mata kwallo ko da daya ba, in ban da bugun fenarti, lamarin da ya sa '' Bafana Bafana '' laske kofin na shida, a yayin da Zimbabwe ke rike da kofuna shida.
Kungiyar zari-ruga ta Aljeriya ta tsallake zuwa zagayen kwata-fainal na kofin Afirka, bayan da ta samu nasarar ci 22 da 16 a wasan da ta buga da Yuganda a ranar Lahadi a birnin Kampala. Dama ya zame wa kungiyar Rugby din Aljeriya ya sami nasara domin hayewa zuwa zagaye na gaba, saboda kungiyar zari-ruga ta Ghana ta lallasa ta da ci 20-22. Sai dai an yi waje road da Ghana biyo bayan mamaye da Yuganda ta yi da ci 53-10. A wasan na kusa da kusa da na karshe dai, Aljeriya za ta kara da Senegal wacce ta zo a saman teburi a rukunin B, yayin da Yuganda za ta kara da Kenya. Ita kuwa Cote d' Ivoire za ta kece raini ne da Namibiya, yayin da Zimbabuwe za ta yi karon batta da Burkina Faso. Duk da kasar da za ta lashe kofin zarin ruga na Afirka za ta kasance wakiliya ta biyu baya ga Afirka ta kudu da za ta kare martabari nahiyar a gasar cin kofin duniya na Rugby a 2023 a kasar Faransa.
Ana dab da soma wasannin Olympics a Tokyo.
A daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan an fara wasannin Olympics a birnin Tokyo na kasar Japan, kungiyar kwallon kafar Jamus da 'yan kasa da shekaru 23 ta yi wasan sa da zumunci da Honduras a karshen mako, inda aka tashi baram-baram saboda kalaman wariyar launin fata da aka nuna wa mai tsaron bayan Hertha Berlin Jordan Torounariga wanda ke da tushe da Najeriya. Sauran 'yan wasan Jamus sun yanke shawarar barin filin kwallo mintuna biyar kafin karshe a lokacin da ake 1-1. Ko da kocin Jamus Stefan Kuntz, sai da ya ce ya zama dole su nuna goyon baya ga Torounariga. "Cikin kankanin lokaci muka fahimci abin da ya faru. Wannan lamarin wani abu ne da ya sabawa kimarmu. Ba za mu iya kyalewa mu yi kamar ba wani abun da ya faru ba; muna son kare dukkan 'yan wasanmu, don haka muka yanke shawarar fita daga filin. Bayan muka sanar da alkalin wasa da kungiyar da muke faftawa da ita, muka yi abin da ya dace. "
Tuni dai kungiyar ta Honduras ta fada a shafinta na Twitter cewa abin da ya faru "rashin fahimta ne a filin wasa", lamarin da ya kasa gamsar da tawagar 'yan kasa da shekaru 23 na Jamus. Wasan farko na Jamus a gasar Olympics zai gudana ne da Brazil ranar Alhamis, kwana daya kafin a bude gasar a hukumance.
A birnin Tokyo inda wasannin Olympics za su gudana, ana ci gaba da fargabar yaduwar annobar corona bayan da aka gano sababbin 'yan wasa da suka kamo da kwayar cutar, ciki har da 'yan wasa biyu na kungiyar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu da kuma memba daya na gudanarwa. Hakazalika, an tilasta wa 'yan wasan Birtaniya shida da ma'aikata biyu kebe kansu lokacin da suka isa Japan bayan da suka hadu da wani mutum da ya kamu da corona. Wannan bazuyar corona na damun wasu 'yan Japan, musamman wadanda suka nemi a soke gasar gasar saboda matsalolin tattalin arziki da kasar ke ciki a wannan yanyi na matsalar kiwon lafiya da duniya ke fuskanta.
An kammala gasar Tour de France
Dan tseren kasar Sloveniya mai suna Tadej Pogacar ya lashe karo na 108 na tseren keken mafi shahara a duniya na Tour de France a wannan Lahadin a birnin Paris. Kasancewar ya taba zama zakaran tsaren a shekara ta 2020, wannan ya zama karo na biyu kenan da dan wasan mai shekara 22 ya zama gwanin Tour de France. Wanda ya zo na biyu a tseren shi ne Dane Jonas Vingegaard wanda ya halarci tseren keken a karon farko, inda ya samu tazarar fiye da minti biyar da wanda ya zo na daya. Rabon da a samu irin wannan rata tsakanin na biyu da na farko a Tour de France tun daga 2014, lokacin da 'yan tseren keke Vincenzo Nibali da Jean-Christophe Péraud suka zo na daya da na biyu.