1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Laberiya: George Weah ya lashe zabe

Ramatu Garba Baba
December 28, 2017

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya George Weah ya lashe zaben shugaban kasar Laberiya da kashi 61.5 cikin dari na kuri'un da aka kada a zagaye na biyu na zaben da ya gudana a ranar Talatar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/2q4d8
Libera, George Weah
Hoto: Getty Images

An dai fafata a tsakanin mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai da George Weah bayan jinkirin da aka samu a sanadiyar zargin da dan takara da ya zo na uku ya yi na cewa an tafka magudi. Daga bisani kotu ta yi watsi da koken tare da tsayar da ranar ashirin da shida na wannan watan na Disamba don gudanar da zaben.

Majalisar Dinkin Duniya  da sauran kungiyoyin kasa da kasa da suka sa ido kan zaben, sun yabawa 'yan kasar kan yadda suka gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Yanzu Weah shi zai gaji shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf mace ta farko da ta zama shugaba a Afrika wadda kuma ta shafe shekaru 12 tana mulkin kasar ta Laberiya.