Kwayar cutar Corona virus, ta fara bulla ne a kasar China a wata kasuwar kifi da ke kasar mai suna Wuhan. Tana ci gaba da bazuwa a sassan duniya inda ta lakume rayuka jama'a wajen 450. Cutar na yaduwa ne ta hanyar cudanya da mai dauke da kwayar, yayin da kuma gane wanda yake dauke da ita da wuri ke da wahala. Tana tana farawa ne, ta hanyar kamuwa da zazzafar mura da zubar jini kafin ta yi illa.