1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lagos za asake bude jami'o'i da manya-manyan makarantu

Abdoulaye Mamane Amadou
August 30, 2020

Hukumomi a jihar Lagos Najeriya sun bayyana ranar 14 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a sake bude jami'o'in kasar da sauran manyan makarantun boko watanni bayan rufe su saboda annobar Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3hmOM
Nigeria Abuja 2014 | Studenten & Ergebnis der Prüfungen
Hoto: Imago Images/Xinhua Afrika

An bayyana ranar 14 ga watan da ke tafe a matsayin na bude manyan jami'o'in jihar da ke Najeriya da sauran makarantun da ake koyar da ilimi mai zurfi, hukumomin jihar sun kuma ayyana ranar 21 ga watan na gobe a matsayin ranar da makarantun firamarai da sakandarai za su sake budewa a matsayin gwaji.

A baya daliban manya-manyan makarantun Najeriya sun gudanar da zanga-zanga don yin kakkausar suka game da matakin gwamnati na ci gaba da kulle makarantun bokon kasar saboda Coronavirus.

Gwamnatin kasar na shirin sake bude filayen jiragenta ga kasashen waje a ranar biyar ga watan Satumba bayan sake dage ranar bisa wasu dalilai.