COVID-19: Fargabar rashin tsaro a Lagos
April 17, 2020Rundunar 'yan sandan jihar ta Lagos ta bakin kakakinta DSP Bala Elkhana ta tabbatar da cewa,wannan batun ba shi da tushe balle makama, ta ce koda a wata biyun da suka shude sai da aka cafke a kalla sama da 'ya'yan kungiyar 800, inda aka gurfanar da su a gaban kotu, kuma a yanzu haka suna gidan kaso. 'Yan kungiyar dai na taruwa ne a Igando, inda daga nan suke kwarara zuwa Sango Ota da ke jihar Ogun.
A duk inda ka zaga a jihar ta Lagos dai, jami'an sojoji da sauran jami'an tsaro ke sinturi a kan hanyoyi domin tabbatar da tsaro da kuma ganin an bi dokar zaman gida sau da kafa. Bincike dai ya nuna cewa a jihar ta Lagos idan har mutum yaki zaman gida, to babu shakka zai iya haduwa da fataken dare kuma su daka masa wawa su kwace duk abin da yake dauke da shi.