1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Armin Laschet ya zama shugaban jam'iyyar CDU

Abdoulaye Mamane Amadou MAB
January 16, 2021

Bayan fafatawa tsakanin 'yan takara, gwamnan jihar NRW Armin Laschet, ya yi nasara a zaben shugabancin jam'iyyar CDU. Abin jira a gani shi ne ko yana so ko kuma za a ba shi damar takarar shugabancin gwamnatin Jamus.

https://p.dw.com/p/3o0u4
CDU Digitaler Parteitag Laschet wird Vorsitzender
Hoto: Hannibal Hanschke/REUTERS

Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ta zabi gwamnan Nordrhein-Westfalen Armin Laschet  a matsayin sabon shugabanta, a yayin babban taron jam'iyyar da take shirye-shiryen kammalawa a karshen wannan mako.

Da gagrumin rinjaye ne dai wakilan jam'iyyar CDU suka zabi Armin Laschet mai shekaru 59 a duniya, da kuma ake yi wa kallon mai ra'ayin ci gaba da manufofin Angela Merkel, inda ya samu kuri'u 521 a gaban abokin hamayyarsa, kuma mai rajin sauyi Friedrich Merz da ya samu kuri'u 466.

Ana sa ran nan ba jimawa ba, sauran membobin jam'iyyar su kada kuri'unsu, wanda hakan ke a matsayin wata kafa kawai ta tabbatar da zabin da wakilan jam'iyyar suka riga suka yi.