'Yan gudun hijira cikin rudu a Lesbos
September 10, 2020A ra'ayin Jannis Papadimitriou na tashar DW, lokaci ya yi da EU za ta samar da ingantattun wuraren zama ga rukunin irin wadannan mutanen da suka rasa matsugunnensu, saboda wasu dalilai. A shekara ta 2016 da 2019 ma an samu gobara a sansanin, sai dai a wannan karon wutar ta yi muni saboda wata iska mai karfi da ke tafiyar kilomita 70 cikin tsukin sa'a guda. Hankalin jami'an kashe gobara ya karkata ne zuwa wutar jejin da ke ci gaba da ci a wasu yankuna.
Karin Bayani:Jamus na kira ga EU a kan daukar 'yan gudun hijira
Jannis Papadimitriou ya ce: Har yanzu ba mu sani ba ko gobara ce, ko sakaci ko kuma kawai wata mummunar ƙaddara ce ga dubban mutanen da aka jibge a sansanin da suke kira matsugunansu. Mun san da cewar an cunkusa mutane 13,000 a wurin da aka tanadarwa mutane 2,500, ba zai tsallake makomar irin wannan bala'in ba.
Tuni dai wadannan 'yan gudun hijira da sauran 'yan uwansu ke kiran sansanin na Moria da sunan "Abin kunyar Turai", kazalika abin kunyar Girka. Moria ya kasance matattarar da gwamantin Athen ke tsugunar da 'yan gudun hijira. Sai dai kuma rufe wurin na nufin, samarwa 'yan gudun hijirar matsugunnai a wani wurin na daban.
Karin Bayani: Turai da sabon rikicin'yan gudun hijira
Amma babu alamun niyyar yin hakan, duk da cewar Girkar ta karbi tallafin biliyoyin Euro daga kungiyar EU, domin ta yi amfani da su wajen tallafawa 'yan gudun hijira da ke shiga kasar. Duk da alkawura masu yawa, sai dai babu gwamnatin Athens da ta cimma nasarar aiwatar da shirin bai wa 'yan gudun hijirar mafakar siyasa. Wajibi ne sababbin shiga kasar su yi jiran shekara guda kafin su samu izinin ganawa da jami'an da ke lura da bayar da mafakar. Sai dai wannan ba laifin Girkar ba ne ita kadai. Tsawon lokaci kena kasashen Turan suke nuna halin ko oho. Tambayar ita ce: Me kungiyar ta EU ke yi?
Karin Bayani: Rikicin 'yan gudun hijira a kasashen EU
A halin da ake ciki yanzu, duk da umurnin hukumar gudanarwa, kasashe wakilai na ci gaba da yin biris da aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da sauran kasashen kungiyar. Illar hakan ita ce, a sauwake gwamnatocin Turan kan yi watsi da irin wadannan sharudda a matakin kungiya da ma hukuncin kotun Turan, tare da dora laifin rashin cimma nasara akan Brussels.
Tsawon shekaru dai ake yayata hotuna masu tayar da hankali dangane da yadda rayuwa take a sansanin 'yan gudun hijirar na Moria, kuma duk wanda ya ga hotunan tabbas ba sai an fada masa yadda irin wannan wuri zai yi doyi ba.
Karin Bayani: Rikicin Turai da Turkiyya kan 'yan gudun hijira
Akwai tarin sharar rubabbun abubuwa a ko'ina cikin sansanin na Moria ga hayaki daura da wariri iri-iri, wanda ka iya kai mutum kusa da kabari da ya zamewa dubban mutane tilas su kwana su tashi da shi a kullum. Shin wannan shiri ne na jami'an EU na yin hannunka mai sanda ga 'yan gudun hijirar da ke keta teku da sunan neman tudun mun tsira a Turai? Idan kuwa haka ne, to wannan shiri bai samu nasara ba. Mutanen da yaki ya ritsa dasu a Siriya da Afghanistan da sauran kasashe ba su da wani zabi face wannan zaman jiran gawon shanun a tsibirin na Girka, ba tare da la'akari da munin yanayin rayuwar wurin ba.