1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira sun tagaiyara a Lebos

Usman Shehu Usman ATB
September 15, 2020

Dubban ‘yan gudun hijira a tsibirin Lesbos sun shiga halin tagaiyara sakamakon gobara da ta kone sansanin da aka stgunar da su na Moria. ‘Yan gudun hijirar na watangariri a tsananin zafin rana da yunwa.

https://p.dw.com/p/3iVD7
Griechenland Flüchtlinge Lesbos
Hoto: Getty Images/AFP/L. Gouliamaki

Lamarin dai ya faru ne bayan gobarar da ta kone daukacin sansanin 'yan gudun hiran kurmus. Don haka tilas dubban 'yan gudun hijirar suke kwana a filin Allah. Cornille Ndama dan gudun hijira ne daga Jamhuriyar Demokradiyar Kwango, wanda lamarin ya shafa.

"Mun rasa komai, dagani sai rigar jikina. Bani da komai tare da ni, kuma bamu san inda zamu samu wajen kwanciya ba"

Haka shi ma wannan dan gudun hijirar daga Afganistan Yiagio Mousavid.

 "Ina dukkanmu za mu kwanta, babu abinci, ba ruwa, babu kudi"

Griechenland, Lesbos I Moria I Kara Tepe
Hoto: Getty Images/AFP/L. Gouliamaki

A halinda ake ciki dai hukumomi sun dora alhakin tashin gobarar a kan 'yan gudun hijira da ke a fusace, kan yadda aka takurasu suka guje ma yaki sannan ga annobar korrona kamar yadda Firaministan Girka Kryiakos Mitsotakis ke cewa.

"Na san irin tsaninin da suke ciki. Amma kuma babu wani uzuri da za a bayar wajen kare lafiyar jama'a, musamman ga irin wannan mummunan tashin hankali"

 A halin da ake ciki dai an fara kwaso yara 400 ‚yan gudun hijira wadanda ba sa tare da iyayensu. Ga sauran 'yan gudun hijirar kuwa makomarsu na hannu gwamnatocin Turai, kuma babu tabbas abin da ka iya faruwa.