Likitan da ya kwarmata cutar Corona ya rasu
February 7, 2020Talla
Daya daga cikin likitoci wadanda suka fara yekuwa game da kwayar cutar coronavirus ya rasu a sakamakon kamuwa da cutar a Wuhan.
Sai da ‘yan sanda suka ja kunnen likitan Li Wenliang saboda abin da suka kira yada labaran karya da ya yi game da cutar a watan Disamba. Yana daga cikin jami’an lafiya su takwas wadanda aka zarga da yada labaran karya game da kwayar cutar.
A wannan Juma’ar ce asibitin da aka kwantar da likitan a Wuhan ya sanar da mutuwarsa. Hukumar lafiya ta duniya ta baiyana ta’aziyarta a wani sako da ta wallafa a shafin Twitter.
Adadin mutanen da suka rasu a sakamakon cutar a China ya karu zuwa 636 yawancin su a lardin Hubei inda aka fara gano bullar cutar.